Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar wani mutum a wurin aikin gini

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta tabbatar da mutuwar, Nwanne Ogbonaya wani lebura mai shekaru 45 bayan bulo ya faɗo masa a wurin aikin gini.

Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin ya faɗawa kamfanin Dilalancin Labaran Najeriya NAN a Lagos cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 04:30 a Opebi dake Ikeja.

Hundeyin yace yayan marigayin ne ya kai rahoton faruwar lamarin ofishin ƴan sanda.

A cewarsa Ogbonaya na aiki ne a wurin wani gini da ake rushe tsoho ake gina wani.

“Kawai sai gini ya faɗo masa yaji masa raunuka ya suma,”

“An garzaya da shi asibitin koyarwa na jami’ar Lagos inda likita ya tabbatar da mutuwarsa,” a cewar Hundeyin.

Ya ƙara da cewa ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

More News

Gwamnatin Enugu ta bayyana dalilin sanya haraji kan gawar mutane

Gwamnatin Jihar Enugu a ranar Lahadi tayi ƙarin haske kan matakin da ta ɗauka kan sanya haraji akan gawar mutane dake ajiye a ɗakin...

Ɗan tsohon gwamnan Kaduna Ahmad Makarfi ya rasu a hatsarin mota

Faisal Makarfi dan gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmad Muhammad Makarfi ya rasu. Faisal ya rasu a wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar...

Ƴan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da kisan kai da fashi da makami a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce a cikin mako guda  jami'an ta sun kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata fashi...

Ƴan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Gyaran Hali na Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami'an ta sun kama Kyari Kur ɗaya daga cikin ɗaurarrun da suka tsere daga gidan gyaran hali ...