Rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja, ta ce jami’an rundunar sun samu nasarar kama wasu mutane 6 da ake zarginsu da aikata fashi da makami.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar mai magana da yawun rundunar,Josephine Adeh ta ce an kama mutanen ne ranar Laraba a wani ginin asibiti da ba a kammala ba a yankin Utakpo dake birnin.
Adeh ta ce an samu mutanen ɗauke da ƙaramar bindiga ƙirar gida da kuma wani abu da ake zargin cewa ganyen tabar wiwi ce.
Wasu daga cikin mutanen sun fito ne daga jihohin dake makotaka da Abuja.
Karin binciken da aka gudanar kan harsashin dake cikin bindigar ya kai ga kama ga kama wani mai suna Yusuf Iliyasu wanda ake kira da Tablet da ya kasance tsohon mai aikata laifi kuma shi ne jagoransu.