Ƴan sanda sun kama wasu ɓarayin wayar wuta

Jami’an bijilante a jihar Legas sun samu nasarar kama wasu ƴan uwa biyu dai-dai lokacin da suke sace wayar wata na’urar bada hasken wutar lantarki wato taransifoma.

An kama mutanen ne a layin Onitiri dake unguwar Abule-Egba a birnin na Lagos.

Bayan kama su jami’an na bijilante sun miƙa su ofishin ƴan sanda na Oko-Oba.

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ce ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta X da aka fi sani da Twitter a baya.

More News

Zanga-zanga: An jibge ƴan sanda 4200 a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tura ƴan sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haƙuri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...