Ƴan sanda sun kama wasu ƴan fashi da makami 5 a Bauchi

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta ce jami’anta sun  kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata fashi da makami a ƙaramar hukumar Misau dake jihar.

A wata sanarwar da aka fitar ranar Talata mai magana da yawun rundunar, Ahmad Wakili ya ce waɗanda ake zargin sun haɗa da Ahmad Musa, wanda ake kira  Abba Yausa, mai shekaru 20; Tijjani Abdullahi, da ake kira da T.J. mai shekaru 20; and Danladi Aliyu, da aka fi sani da Uban Daba, mai shekaru 30.

” Duk da cewa lamarin ya faru a cikin watan Yuli 2024 lokacin da waɗanda ake zargin tare da wasu mutane huɗu Ismail Kawuwa, Sadiq Kange, Adamu Dan Kamfani, da kuma Attahir wanda ake nema ruwa-a-jallo sun haɗa baki inda suka haura gidan wani da ake kira Malumi a garin Misau dake jihar Bauchi,” ya ce.

“Ɗauke da ƙaramar bindigar fistol ƙirar gida da harsashi guda 7 sun yiwa Malami fashin ₦250,000 wayoyin hannu guda uku da katunan waya na kamfanoni da dama ba a san adadin kudinsu ba,”

Sanarwar ta ce Ahmed Musa shi ne wanda aka kama da bindigar inda bayan yi masa  tambayoyi ne ya amsa laifin aikata fashin da makamin.

Mai magana da yawun rundunar ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, Auwal Musa ya bayar da umarnin mayar batun sashen binciken manyan laifuka na rundunar.

More from this stream

Recomended