Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami’an Æ´an sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna.

Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan shekara 30 na zaune ne a yankin  Yan Bokolo a Malalin Gabas dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Jami’an Æ´an sandan rundunar Operation YaÆ™i su ne suka kama shi a ranar 21 ga watan Mayu biyo bayan bayanan sirri da suka samu daga Sashen Bayanan Sirri na hedkwatar rundunar Æ´an sanda dake Abuja.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda aka kaman na da alaÆ™a da Dogo Haliru gawurtaccen mai garkuwa da mutane da aka sani da addabar jihohin Zamfara,Katsina da kuma babbar hanya hanyar Abuja zuwa Kaduna.

More News

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...

Sojojin sun kama wani mai safarar bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin  samar da  tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar  bindiga da ake nema ruwa...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akan hanyar Abuja-Kaduna

Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus...

Kotu ta yanke wa É—ansanda hukuncin kisa saboda laifin kisan kai

Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yanke wa Sufeta Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin...