Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami’an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna.

Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan shekara 30 na zaune ne a yankin  Yan Bokolo a Malalin Gabas dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Jami’an ƴan sandan rundunar Operation Yaƙi su ne suka kama shi a ranar 21 ga watan Mayu biyo bayan bayanan sirri da suka samu daga Sashen Bayanan Sirri na hedkwatar rundunar ƴan sanda dake Abuja.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda aka kaman na da alaƙa da Dogo Haliru gawurtaccen mai garkuwa da mutane da aka sani da addabar jihohin Zamfara,Katsina da kuma babbar hanya hanyar Abuja zuwa Kaduna.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...