
Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta kama wani mai suna,Orji Isaac ɗan shekara 67 da aka samu da laifin sayar da miyagun kwayoyi a jihar.
Jami’an rundunar yan sandan jihar sun kama wanda ake zargin ne a yayin wani samame da suka kai yankin Yaba a ranar Laraba.
Benjamin Hundeyin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce an kama wani mai suna Lekan Ganiyu ɗan shekara 22 a lokacin da yake sayan ƙwayar a wurin mutumin da aka kama.
Za a gurfanar da mutanen biyu gaban kotu bayan kammala bincike.