Ƴan sanda sun kama mutane 4 masu garkuwa da mutane a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta ce jami’an tsaro sun kama wasu mutane huɗu da ake zargin ƴan fashin daji ne dake addabar birnin.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan birnin, Josephine Adeh ta ce an kama mutanen ne a ranar 7 ga watan Yuni a yayin wani samamen haɗin gwiwa da ya haɗa da sojojin dake tsaron fadar shugaban, jami’an DSS, mafarauta da kuma ƴan sanda.

Adeh ta ce jami’an tsaro sun yi amfani da bayanan sirri inda suka farma wasu sanannun sansanin masu garkuwa da mutane dake Gidan Dogon da kuma Dajin Kweti dake Kaduna kan iyaka da Abuja inda suka bi sawun mutanen suka kuma kama su.

Ta ce mutanen da aka kama sun haɗa da Yahaya Abubakar mai shekaru 25; Mohammed Mohamed, mai shekaru 32, wanda tsohon mai laifi ne ; Umar Aliyu, mai shekaru 20; da kuma  Nura Abdullahi mai shekaru 32 wanda shima tsohon mai laifi ne.

Mutanen sun amsa laifin kasancewa mambobi na ƙungiyar masu garkuwa da mutane da sukewa kansu laƙabi da ‘Mai One Million’ wanda su ne da alhakin garkuwa da mutane da dama Abuja da kewayenta.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...