Ƴan sanda sun kama mai garkuwa da mutane da ya kashe ɗan gidan ASP na ƴan sanda

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta kama wani mai suna, Rabi’u Adamu da ake zargi da yin garkuwa da kuma kisan wani yaro ɗan shekara 12 ɗan gidan ASP Bala Yarima.

A wata sanarwa ranar Juma’a, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar,Ahmed Wakili ya ce wanda ake zargi mai shekaru 21 ya yi garkuwa tare da kashe Christopher Musa dake garin Magaman Gumau.

Wakili ya ce anyi garkuwa da marigayin ranar ranar 21 ga watan Maris lokacin da aka aike shi.

” A ranar 21 ga watan Maris 2024 da ƙarfe 08:00 na safe rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta samu kiran kai ɗaukin gaggawa na yin garkuwa da Christopher Bala ɗan gidan ASP Bala Yarima a garin Gumau,” a cewar sanarwar.

Biyo bayan binciken farko da aka yi wanda ake zargin ya amsa laifin shaƙe wuyan Christopher har ya mutu kuma ya amsa laifin  tatsar kuɗi har naira 200,000 daga mahaifin yaron.

Wanda ake zargin ya ce bayan da ya fuskanci cewa marigayin ya gane shi hakan ne ya sa ya kashe shi inda ya binne shi kusa da wani tsauni dake ƙauyen Bazale.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum ɗaya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faɗa tsakanin ƴanbindiga da ƴanbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...