Ƴan sanda sun kama dan damfara a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani da ake zargin dan damfara ne da ya kware wajen damfarar jama’a wadanda ba su ji ba gani ba ta hanyar amfani da kudin jabu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Sadiq, ya ce ‘yan sanda sun samu nasarar cafke wanda ake zargin, Bishir Umar mai shekaru 28, wanda aka fi sani da Dan Zamfara daga karamar hukumar Magamar Jibia, a lokacin da rundunar ta samu bayanan sirri kan ayyukansa da kuma inda ya ke.

“Bayan an binciko shi nan take aka kama shi, an kwato wasu kudade na jabu daga hannun sa, guda hudu na N1000, CFA 10,000 na jamhuriyar Nijar, da takardar 2000 na CFA na jamhuriyar Nijar,” in ji ASP Sadiq.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, ya ce wanda ake zargin a yayin gudanar da bincike, ya amsa laifin aikata laifin.

More from this stream

Recomended