Ƴan sanda sun kama Chinaza Philip ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

Ƴan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane wanda ake kira da Chinaza Philip.

Rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja ta karbi Chinaza bayan da rundunar yan sandan jihar Kaduna ta miƙa mata shi.

Jami’an yan sanda ne suka kama shi a Kaduna ranar Alhamis akan hanyarsu ta zuwa Kano ɗauke da wani mutum da suka yi garkuwa da shi daga Abuja.

More from this stream

Recomended