Rundunar Ƴan Sandan Najeriya ta ce jami’anta sun kwashe wasu nakiyoyin da abubuwan fashewa a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, Olumuyiwa Adejobi mai magana da yawun rundunar ya ce tawagar rundunar ƴan sandan dake lura da kwance bam ne suka kwashe nakiyoyin.
Adejobi ya ce mazauna yankin ne suka ankarar da jami’an tsaro bayan da suka ga bama-baman a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce shida daga cikin abubuwan fashewar an gano su ne a yankin Dala Kachalla a kusa da wani gini da ba a kammala ba.
“Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ruwan da aka yi ce ta bankaɗo su a yayin da ƴan gwangwan su ka yi watsi da su,” a cewar sanarwar.
Har ila yau an samu nasarar gano wasu bama-baman a bakin ruwa dake Gwangwe.