Ƴan Sanda Sun Ceto Mata Da Mijinta Daga Hannun Ƴan Fashin Daji A Katsina

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce jami’anta sun samu nasarar daƙile wani hari da ƴan fashin daji suka kai ƙauyen Hayan Dam dake ƙaramar hukumar Kankara ta jihar.

A wata sanarwa ranar Laraba, mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Aliyu Abubakar ya ce ƴan fashin dajin sun farma garin ne ɗauke da muggan makamai.

Aliyu ya ce jami’an rundunar sun yi bata kashi da ƴan bindiga har ta kai ga sun ce to mutane biyu mata da miji da aka yi niyar garkuwa  su.

A ranar Litinin ne da misalin  ƙarfe 09:45 na dare maharan suka kai farmaki gidan wani mai suna Kabiru Magaji dake ƙauyen Hayan Dam a ƙokarinsu na yin garkuwa da shi tare da matarsa Sa’adatu Magaji.

Sanarwar ta ƙara da cewa gaggawa da DPO na Kankara ya yi wajen tura jami’an ƴan sanda bayan samun labarin ita ta  haifar da samun nasarar ceto mata da mijin.

More from this stream

Recomended