Ƴan sanda a Jihar Kebbi sun haramta amfani da nok-awut a lokacin bikin Kirsimeti

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Kebbi, ta gargadi mazauna jihar game da yin wasan wuta da bugun nok-awut a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, SP Nafiu Abubakar ya sanya wa hannu.

Abubakar ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda, CP Chris Aimionawane, ya himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ya ce, “A cikin ƙudirinsa na dorewar yanayin zaman lafiya da aka riga aka wanzar a lokacin Kirsimeti, Kwamishinan ‘yan sandan Rundunar Jihar Kebbi, CP Chris Aimionowane, ya yi magana a yau, Juma’a, 22 ga Disamba, 2023, ya kuma gana da kwamandojin yankin, don ƙarfafa tsarin yanayin tsaro a kusa da cibiyoyin addini da nishaɗi a faɗin jihar.”

More from this stream

Recomended