Kwamishinan ƴan sandan jihar Anambra, Obono Itam ya ce an ceto wasu yara huɗu da aka sato su daga wurin iyayensu a jihar Bauchi aka kuma sayar da su ga wasu iyalai a jihar Anambra.
Kwamshinan ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da yake ganawa da ƴan jaridu a hedkwatar rundunar a Awka babban birnin jihar kan ayyukan rundunar a shekarar 2024.
A yayin ganawar an gabatar da wasu mutane 13 da ake zarginsu da kisan kai, fashi da makami da kuma sauran laifuka a jihar.
Mutane huɗu aka kama da hannu a safarar yaran ciki har da wata da take fakewa da cewa ita marikiyar yaran ce.
Itam ya tabbatar da cewa tuni iyayen ɗaya daga cikin yaran suka gane shi kuma ana cigaba da ƙoƙarin haɗa sauran yaran da iyayensu.