Wannan ba shi ne lokacin jin daɗi ga masu iyalai Najeriya ba, waɗanda suka ɗauki tsauraran matakan rage tsada don jure wahalhalun da aka fuskanta kwanan nan sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka.
Shinkafa, wadda za a iya cewa tana daya daga cikin kayan abinci da ake amfani da su a kasar nan sosai, ta kai Naira 77,000 kan kowane buhu.
A cikin watan Disamba, Hukumar Kididdiga ta kasa ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a kasar ya kai sama da shekaru 27 ana fama da shi yayin da farashin kayayyaki ya karu zuwa kashi 28.9 cikin dari.
An samu hauhawar a watan Disamba wanda ya nuna karuwar kashi 0.72 idan aka kwatanta da na watan da ya gabata.
A shekarun baya-bayan nan dai farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a fadin Najeriya.
Lamarin dai ya tabarbare ne sakamakon tasirin manufofin gwamnati da suka hada da cire tallafin man fetur da faduwar naira a kasuwar canji.