
Yan majalisar dokokin jihar Rivers 27 ne cikin 32 suka sauya sheka daga jam’iyar PDP mai mulkin jihar ya zuwa jam’iyar adawa ta APC.
Ƴan majalisar sun sauya shekar ne a cikin wani hoto da suka ɗauka tare suna riƙe da tutar jam’iyar APC.
Sun bayyana cewa rabuwar kai da aka samu a cikin jam’iyar PDP shi ne babban dalilin su na sauya shekar.
Wannan cigaban da aka samu zai kara ruruta rikicin siyasar da ake fama da shi a jihar tsakanin tsohon gwamna, Nyesom Wike da kuma gwamna mai ci Siminalayi Fubara.