Ƴan Fashin daji sun kashe sojoji 4 a Zamfara

Edward Buba daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar tsaron Najeriya ya ce sojoji huɗu ƴan ta’adda suka kashe ranar Lahadi a wani harin kwanton ɓauna da aka kai musu.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Buba ya ce sojojin sun fuskanci hare-haren kwanton ɓauna har sau biyu daga ƴan fashin daji a ƙauyen Kuran Mota da kuma a kan hanyar Alikere zuwa Yarmalimai dake jihar ta Zamfara.

Ɓuba ya ƙara da cewa sojoji uku sun jikkata a harin.

Ya ce sojojin sun samu nasarar kashe wasu daga cikin ƴan ta’addar biyo bayan da tallafin dakarun sojan sama da suka samu a lokacin fafatawar.

” A ranar 12 ga watan Mayu dakarun rundunar Operation Hadarin Daji sun fuskanci harin kwanton ɓauna sau biyu daban-daban ɗaya a ƙauyen Kuran Mota da kuma akan titin Alikere-Yarmalimai  a jihar Zamfara,” a cewar sanarwar.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...