Ƴan fashin daji sun kashe ɗan sanda ɗaya a wani shingen bincike a Zamfara

Ƴan fashin dajin a ranar Lahadi sun kai da farmaki kan wani shingen binciken ƴan sanda inda suka kashe ɗan sanda guda ɗaya tare da jikkata Wasu.

Shingen binciken an kafa shi ne tazarar  ƙasa da kilomita ɗaya kafin ka isa Kwatarkwashi garin dake kusa da Gusau babban birnin jihar.

Majiyoyi da dama sun faɗawa jaridar Daily Trust cewa ƴan fashin dake kan babura sama da 40 sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 04:00 na asubahin ranar Lahadi.

Ƴan fashin sun ƙona duk wani mai muhimmanci da suka samu a shingen binciken kafin su  bar wurin.

A cewar wata majiya ƴan fashin dajin sun samu nasarar fin ƙarfin ƴan sandan abun da yasa wasu daga cikinsu suka tsere bayan an ɗauki lokaci suna musayar wuta.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum ɗaya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faɗa tsakanin ƴanbindiga da ƴanbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...