Ƴan Boko Haram sun yi garkuwa da wani alƙali da matarsa a jihar Borno

Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da alƙalin babbar kotu mai Shari’a, Haruna Mshelia tare da matarsa da kuma dogarinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin akan hanyar  Buratai zuwa Buni-Gari a lokacin yake kan hanyarsa ta dawowa daga birnin Maiduguri inda yake aiki.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigar sun fito ne daga cikin daji inda suka rufe titin.

Wata majiya ta bayyana cewa duk da ƙoƙarin da direban ya yi na tserewa  wasunsu sun sake fitowa inda suka sha gabansu suka tsayar da su kana suka tasa ƙeyar mutanen da suke cikin motar ya zuwa cikin Dajin Sambisa.

Titin da lamarin ya faru  shi ne ɗaya tilo daya haɗa kudancin jihar Borno da kuma Maiduguri babban birnin jihar..

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso ya tabbatar da faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended