Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata alƙaliya da ƴaƴanta huɗu a Kaduna

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mai Shari’a Janet Galadima Gimba  tare da ƴaƴanta huɗu a jihar Kaduna.

Alƙaliyar tare da ƴaƴanta anyi garkuwa da su ne daga gidansu dake yankin Mahuta a Kaduna ranar 23 ga watan Yuni.

Masu garkuwar da yawansu ya kai 15 sun mamaye gidan mai shari’ar da daddare lokacin da mijinta wanda likita ne yake wurin aiki.

Da take mayar da martani kan lamarin a ranar Laraba Gloria Ballason babbar jami’ar gudanarwar ƙungiyar House Of Justice tayi kira da a bawa alƙaliyar kariya ita da iyalin ta.

Ballason ta ce masu garkuwar sun kashe, Victor  Gimba ɗan alƙaliyar mai shekaru 14 a ranar 02 ga watan Yuli.

Kawo yanzu ƴan fashin dajin sun buƙaci a biya su miliyan 300 a matsayin kuɗin fansa inda suka yi alkawarin fara kashe mutanen ɗaya bayan ɗaya matuƙar aka samu jinkirin biyan kuɗin.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna,Mansir Hassan ya tabbatar da faruwar.

More News

An gano gawarwakin ƴan fashin daji 8 a Kaduna

Gawarwaki 8 da ake zargin na ƴan fashin daji ne aka gano bayan da sojoji suka kai farmaki dazukan dake ƙauyen Kurutu dake kusa...

Tinubu ya karɓi Anyim Pius a jam’iyar APC

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa  tsohon shugaban majalisar dattawa,Anyim Pius Anyim maraba da zuwa  jam'iyar APC. A makon daya gabata ne Anyim...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...