Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane 5 tare harbe wani jigon jam’iyar APC

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane biyar mazauna ƙauyen Yangoji dake ƙaramar hukumar Kwali a birnin tarayya Abuja suka kuma harbi wani jigo a jam’iyar APC, Alhaji Musa Majaga.

Wani mazaunin Yangoji da ya  bayyana kansa da Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 12:23 na dare lokacin da masu garkuwar suka farma gidan ɗan siyasar.

Ya ce masu garkuwar sun ɓalle ƙarfen tagar gidan Maijaga inda suka shiga ɗaki suka harbe shi tare da yin awon gaba da ƴaƴansa biyu.

” Bayan da suka ɗauki ƴaƴansa biyu sun wuce wani gidan inda suka ɗauke wasu maƙota uku,”ya ce.

Wani ɗan bijilante da yayi magana da wakilin jaridar Daily Trust da ya ziyarci garin ya bayyana cewa masu garkuwar sun yi amfani da damar ƙarancin harsashi da ƴan bijilanten suke fuskanta wajen kai harin.

“Kasan cewa masu garkuwar sun yi amfani da damar bayan da suka samu labari cewa ƴan bijilante suna fuskantar ƙarancin harsashi.Bamu fuskanci harin masu garkuwa da mutane ba a cikin watanni biyar da suka wuce anan Yangoji,”ya ce.

Ya ce jigon APC da aka harba a ƙafa an kai shi wani asibiti mai zaman kansa dake Gwagwalada.

More from this stream

Recomended