Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane 26 a Katsina

Aƙalla mutane 26 ƴan bindiga suka yi awon gaba da su daga garin Runka dake ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Aliyu Abubakar Sadiq mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina shi ne ya tabbatar da faruwar haka ga jaridar The Cable a ranar Talata.

“Ya ce harin ya faru a garin Runka a ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina da ƙarfe 2 na daren ranar Litinin,” ya ce.

“Wasu daga cikin ƴan fashin dajin na sanye da hijabi kuma sun yi garkuwa da kusan mutane 26 maza da mata.”

Mai magana da yawun rundunar ya ƙara da cewa suna cigaba da gudanar bincike kan harin.

Safana na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin dake fama da matsalar ƴan fashin daji da ta addabi jihar.

More from this stream

Recomended