Ƴan bindiga sun sace wasu ɗalibai a jihar Delta

Rahotanni na cewa ƴan bindiga sun sace dalibai da kawo yanzu ba a san yawan adadinsu ba akan babbar hanyar east-west a ƙaramar hukumar Ughelli ta jihar Delta..

A cewar jaridar The Cable ɗaliban dake cikin mota ƙirar Sienna na kan hanyarsu ta dawowa daga birnin Calabar ne  na jihar Cross River lokacin da aka farma motar ta su da yammacin ranar Juma’a.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Delta,Bright Edafe shi  ne ya tabbatarwa da jaridar faruwar haka a ranar Litinin.

Edafe ya ce jami’an ƴan sanda na bin sawun masu garkuwar domin kuɓutar da ɗaliban.

Lamarin ya shiga jerin ƙarin yawan ɗaliban da aka yi garkuwa da su a Najeriya.

More News

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...

Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa a kan kudi

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mazaunin kauyen Kajola da ke kusa da Apomu a jihar mai suna Lukman Adejoju bisa...