Ƴan bindiga sun sace wani basaraken gargajiya a jihar Imo

Wasu yan bindiga sunyi garkuwa da Eze Samuel Agunwa Ohiri tsohon shugaban majalisar sarakuna ta jihar Imo.

Rahotanni sun bayyana cewa anyi awon gaba da basaraken ne da tsakar daren ranar Asabar daga gidansa dake karamar hukumar Oraido Mbaitoli.

Yan bindigar da ba a san ko suwaye ba sun dauke basaraken zauwa wani wuri da ba a sani ba kuma kawo yanzu basu tuntubi kowa ba kan batun.

Wani mazaunin garin Orodo ya ce jama’ar garin na cikin zullumi a yayin da wasu da dama suka kaura cewa gidajen su.

More from this stream

Recomended