
Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da Igboayaka Igboayaka shugaban kungiyar matasan Ohanaeze ta OYC a jihar Imo.
Anyi garkuwa da Igboayaka da maraicen ranar Asabar a unguwar Work Layout dake kusa da mahadar titin jami’ar jihar Imo dake Owerri babban birnin jihar.
A wata sanarwa ranar Lahadi Chilos Godsent shugaban majalisar matasan Igbo na ƙasa ya ce ƴan bindigar sunje wurin a motoci biyu ƙirar Sienna da Lexus.
Godsent ya ce tun bayan da aka ɗauke Igboayaka yan uwa da kuma abokansa basu san inda yake ba.
“Tun bayan samun mummunan labarin ƙoƙarin da tarin mambobin kungiyar matasan Ohanaeze, iyalai da kuma abokai suka yi na tuntubarsa ta waya ya ci tura,” a cewar sanarwar..
“Duka wayoyinsa a kashe suke ba jimawa kaɗan bayan faruwar lamarin.”
Da yake mayar da martani kan faruwar lamarin, Henry Okoye mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce ƴan sanda sun kaddamar da bincike domin gano inda yake.
Okoye ya ce rundunar ba ita ta kama Igboayaka ba kamar yadda wasu suke raɗe raɗi.