Ƴan bindiga sun nemi kudin fansa N30m da babura kan ɗan takarar kansila da suka sace a Kaduna

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani dan takarar kansila mai suna Japheth Zarma Yakubu a unguwar Kurmin-Kare da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna, sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 20 da babura biyu domin a sake shi.

Wata majiya ta shaida wa ƴanjarida cewa shugaban ‘yan fashin ya kira ranar Lahadi da karfe 11:45 na safe ta wayar wanda aka sace ɗin ya kuma bukaci ‘yan uwansa da su tara naira miliyan 20, tare da samar musu da babura guda biyu.

Majiyar ta kuma bayyana cewa daya daga cikin ‘yan’uwan wanda abin ya shafa na tattaunawa da ‘yan fashin don ganin ko za a iya rage kudin fansa.

“Danuwan mutumin ya zo ya sanar da mu yadda ya samu damar tattaunawa da shugaban ‘yan fashin kan bukatar rage kudin fansa da ake nema saboda tabarbarewar tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu,” inji majiyar.

‘Yan fashin sun yi awon gaba da shi ne a lokacin da ya je duba gonarsa a makon jiya Alhamis.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, ba a samu damar jin ta bakinsa ba game da faruwar lamarin har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

More from this stream

Recomended