
Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta ce ana zargin wasu ƴan bindiga da laifin kashe wasu yara uku ƴan gida ɗaya suka kuma saka gawarwakin a cikin na’urar firiza a garin Nnewichi dake karamar hukumar Nnewi North ta jihar Anambra.
Tochukwu Ikenga mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce an gano gawar yaran ne a cikin firizar kuma tuni aka ɗauke su aka kai ɗakin ajiye gawarwaki.
Ikenga ya ce rundunar ta ƙaddamar da bincike kan lamarin inda ya ƙara da cewa kawo yanzu babu wanda aka da ake zargi da aikata kisan.
Ya ce Nnaghe Itam kwamishinan ƴan sandan jihar Anambra ya bayar da umarni da a mayar da binciken laifin sashen binciken aikata manyan laifuka dake Awka domin cigaba da bincike.
Ya ƙara da cewa za a sake fitar da wasu ƙarin bayanai nan bada jimawa.