Ƴan bindiga sun kashe wani basarake a jihar Kogi

Wasu ƴan bindiga sun kashe Shagari Ebije’ego   mai girma Onu na Itama basaraken gargajiya dake ƙaramar hukumar Dekina a gidansa dake garin.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun bi sawun basaraken gargajiyar   har gida da yammacin ranar Litinin inda suka harbe shi har lahira.

Mazauna garin sun ce wasu ƴan bindiga sun shiga garin inda suka zarce kai tsaye zuwa gidan marigayin.

“An ga makasan nasa su da yawa a cikin abun hawa ɗauke da makamai sun nufi gidan basaraken dake garin da misalin ƙarfe 09:00 na daren ranar Litinin,”

“Ba jimawa kaɗan muka fara jin harbi daga wajen gidan abun da ya sa mutane suka sa mutane kowa ya yi takansa.”

Kafin rasuwar tasa marigayin shi ne basarake mafi ƙarancin shekaru a ƙaramar hukumar ta Dekina.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka ƴanbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...