Rundunar ƴan sanda jihar Benue ta ce fararen hula 15 da jami’an ƴan sanda biyu ƴan bindiga suka kashe a ƙauyen Ayati dake ƙaramar hukumar Ukum ta jihar.
A wata sanarwa mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Catherine Anene ta ce an kai harin ne a ranar Alhamis.
Ta ce wasu gungun ƴan bindiga ne suka kai farmaki inda suka buɗewa mutanen ƙauyen wuta.
“Ranar 08/08/2024 da misalin ƙarfe 04:30 na yamma dai-dai lokacin da al’amuran yau da kullum ke cigaba da gudana a ƙauyen Ayati, ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benue ƴan bindiga masu yawan gaske sun farma ƙauyen inda suka riƙa harbin kan me uwa da wabi akan mutane,” ta ce.
” Ƴan sandan dake cikin ƙauyen sun mayar da martani cikin gaggawa kuma sun samu nasarar fatattakar ƴan bindigar,”
“Amma kuma mutane 15 sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga kuma an tabbatar da sun mutu bayan da aka kai su asibiti,”
Anene ta ce an ajiye gawarwakin gawarwakin mutanen dana ƴan sandan a babban asibitin Ukum kuma ana cigaba da gudanar da bincike.