Ƴan bindiga sun kashe manoma 5 a jihar Ondo

Aƙalla manoma biyar aka rawaito an kashe a wani farmaki da wasu ƴan bindiga suka kai Ajegunle Powerline dake ƙaramar hukumar Akure North ta jihar Ondo.

Akin Olawolofe  mazaunin garin  da ya sheda abun da ya faru ya ce wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne suka kai hari ɗauke da bindigogi a garin.

Ya bayyana cewa mutanen da aka kashe leburori ne manoma da aka hayo daga jihohin Filato daga Kaduna.

“Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe uku na rana   ranar Talata. Sun riƙa harbin kan me uwa da wabi inda suka kashe biyar daga cikin ma’aikatan mu. Haka suka saba zuwa suna addabar mu tare da yi mana barnar amfanin gona,” ya ce .

” A lokuta da dama muna kai ƙarar su ga gwamnatin jiha da kuma hukumomin tsaro amma babu wani mataki da aka ɗauka domin kawo ƙarshen lamarin.”

Funmilayo Odunlami-Omisanya, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce rundunar ta kaddamar da bincike.

More from this stream

Recomended