
Wasu yan bindiga sun kai hari gidan kwamishinan zaɓe na jihar Kogi dake Lokoja da tsakar daren ranar Alhamis.
A cikin wata sanarwa da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta fitar ta ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 03:30 na dare.
Sanarwar ta ce maharan sun shafe sama da minti 30 suna musayar wuta da jami’an tsaro kafin ƙarin wasu jami’an tsaro su kawo musu ɗauki.
Babu ko da mutum guda da ya rasa ransa a harin sai dai an tafka asarar dukiya ta miliyoyin naira.
Harin na ranar Alhamis na zuwa ne ƴan kwanaki bayan wasu ƴan bindiga suka kai hari ofishin hukumar zabe ta INEC dake jihar.