Ƴan bindiga sun kai hari gidan casu, sun kashe mutum biyu tare da raunata da dama

An samu tashin hankali a gidan rawa na Porsche da ke Oba, karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra, yayin da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kawo hari, inda suka harbe mutum biyu tare da raunata wasu da dama.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a lokacin da wasu ke yin wani abin nishadi a gidan rawan dare.

A cewar shaidun gani da ido, ‘yan bindigar, wadanda aka ce suna shirin yin garkuwa da mai kulob din, sun fara harbi ne ba gaira ba dalili, inda daga baya jami’an tsaro suka mayar musu da martani a wurin taron.

Daya daga cikin shaidun gani da ido da ke kusa da wurin, wanda ya bayyana sunansa a matsayin Emeka, ya shaida cewa, “’yan bindigar sun yi yunkurin yin garkuwa da mai kulob din, amma jami’an tsaro da ke kula da kulob din sun kawo ɗauki.”

More from this stream

Recomended