Connect with us

Hausa

Ƴan bindiga sun buɗe wuta cikin kasuwa sun kashe mutum 21 a Sokoto

Published

on

Gwamna Tambuwal

Rahotanni daga Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya sun ce akalla mutum 21 aka kashe a harin da ƴan bindiga suka kai a yankin Sabon Birni.

Ƴan bindiga sun buɗe wuta ne a lokacin da mutane ke cin kasuwar garin Unguwar lalle, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.

Sun kuma ce mutane da dama ne suka jikkata a harin, waɗanda ke kwance a asibitin garin Sabon Birni, wasu kuma an tafi da su zuwa Sokoto.

Rundunar ƴan sandan jihar ba ta fitar da sanarwa ba game da harin da kuma mutanen da aka kashe.

Amma tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni, kuma yanzu ɗaya daga cikin mai ba gwamnan jihar Sokoto shawara Honarabul Abdullahi Mohammed Tsamaye ya tabbatar da harin na kasuwar Unguwar Lalle.

Ya ce ƴan bindigar sun ɓude wuta cikin kasuwar suna harbi kan mai uwa da wabi inda suka kashe mutane tare da ƙone motoci.

“A takaice mutum 21 aka kashe, wasu sun samu raunika da yawa suna kwance a asibitin sabon birni wasu kuma a Sokoto,” in ji shi.

Sabon Birni na cikin yankunan da ke fama da hare-haren ƴan bindiga a jihar Sokoto, inda a yankin ne kwanan baya aka kashe wasu sojoji a harin kwantan ɓauna.

Gwamnatin jihar Sokoto ta ɗauki matakai na hana cikin kasuwannin mako da katse layukan salula a yankin domin magance matsalar ƴan bindiga.

Matsalar hare-haren ƴan fashi na ci gaba da yin ƙamari a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Duk da Hukumomi na cewa ana samun nasara kan ƴan fashin dajin da ke faɗin jihar, amma kuma ƴan bindigar na ci gaba da kai hare-hare.

Ko a makon nan ƴan bindiga sun abka garin Kuryar Madaro da ke cikin ƙaramar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara inda suka kashe mutane da dama tare da ƙone motoci da gidaje.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending