Ƴaƴan jam’iyyar sun yi tattakin nuna goyon baya ga hukumar INEC a Abuja

0
...

Magoya bayan jam’iyyar All Progressive Congress mai mulkin Najeriya sun gudanar da wani tattaki a birnin Abuja, wanda suka ce sun yi ne domin nuna goyon baya ga demokuradiyya.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peopls Democratic Party, PDP, mai hamayya, Atiku Abubakar ya jagoranci zanga-zangar rashin yarda da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Tattakin, wanda magoya bayan jam’iyyar APC ɗin suka shirya, sun ce sun yi ne domin nuna amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar wanda aka gudanar a watan Fabarairu.

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC, ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar, inda zai gaji shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, wanda ke kammala wa’adin shugabancinsa na biyu na shekara huɗu-huɗu.

Sai dai manyan jam’iyyun adawa, irin su PDP da LP sun nuna rashin amincewa da sakamakon, inda dukkaninsu suka sha alwashin ƙalubalantar sakamakon a kotu.