Ƴaƴan jam’iyyar NNPP sun gudanar da zanga-zanga a Kano domin nuna kin jininsu ga yunkurin da ake na tura sabon kwamishinan yan sanda zuwa jihar.
Kafofin yada labarai da dama sun bada rahoton cewa Babba Sufetan Yan sandan Najeriya ya amince da tura kwamishinan ƴan sanda, Balarabe Sule a matsayin sabon kwamishinan yan sanda na jihar.
Kasancewarsa tsohon shugaban jami’an tsaro na gwamnan Kano, Abdullahi Umar ya sa ƴaƴan jam’iyyar ta NNPP ke zargin cewa an yi haka ne domin shirin murde zaɓen gwamnan jihar.

