Ƙungiyar NLC za ta yi taro don tattauna wahalhalun da ƴan Najeriya ke sha saboda tsadar fetur

Mataimakin sakataren kungiyar ƙwadago ga NLC na kasa, Chris Onyeka, ya ce kwamitin gudanarwa na kungiyar zai yi wani muhimmin taro a yau tare da daukar matsaya kan tsadar man fetur a Najeriya.

Ya ce duk wasu batutuwan da suka shafi wahalhalun da talakawa ke ciki saboda tashin farashin mai na baya-bayan nan, za a duba su a wurin taron.

“Za mu bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adi. Mun ba su isasshen abin da za su kula da ’yan Najeriya su gyara, amma sun ki gyara. Su shirya kansu domin muna shiri. A shirye muke mu yaƙe su,” inji shi.

A halin da ake ciki kuma, kungiyar Kwadago ta yi watsi da shirin bai wa gwamnatocin jihohi damar fitar da kayan agaji ga ‘yan kasa domin rage wahalhalun da suke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur.

Idan ba a manta ba, Shugaban kasa Bola Tinubu a jawabinsa na kaddamarwa a ranar 29 ga watan Mayu ya sanar da kawo karshen tsarin tallafin man fetur wanda nan take ya rufe farashin famfon na Premium Motor Spirit wanda aka fi sani da man fetur daga Naira 165 kan kowace lita zuwa N540.

A halin yanzu ana sayar da man tsakanin N568 zuwa N617 kowace lita.

More from this stream

Recomended