Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice daga taron.

Gwamnatin ta kira taron ne domin tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashi da za a riƙa biyan ma’aikata a Najeriya.

Joe Ajaero shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC da kuma Tommy Okon mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadago ta TUC sune suka wakilci ma’aikata a wurin taron.

Da yake magana da ƴan jaridu a wurin taron Ajaero ya yi allah wadai da tayin biyan  ₦48,000 da gwamnatin tarayya ta yi a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Ya ce gwamnatin ba da gaske take ba kan tattaunawa da take da  ƴan kungiyar ƙwadagon.

Ajaero ya ce gwamnati na da kwanaki har zuwa ƙarshen wannan watan domin ta fitar da matsayarta  kan batun.

Tun da farko ƙungiyoyin TUC Da NLC sun miƙawa gwamnati buƙatar ta riƙa biyan ₦615,500 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...