Ƙuncin Rayuwa:Sai da muka gargaɗi ƴan Najeriya kada za su zaɓi APC – Tambuwal

Tsohon gwamnan Sokoto kuma sanata mai wakiltar mazaɓar Kudancin Sokoto a majalisar dattawa, Aminu Waziri Tambuwal  ya bayyana halin wahalar rayuwa da ake fama da ita ƙasarnan a matsayin illar sake  zabar jam’iyar APC a shekarar 2023.

Da yake magana a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar PDP a Sokoto  ranar Lahadi Tambuwal ya ce “Lokacin yaƙin neman zaɓe a 2023  mun gargadi ƴan Najeriya kada su maimaita kuskuren sake zaɓar jam’iyar APC basu da wani abun arzikin da za su yi wa jama’a ,”

“Mun faɗa musu APC bata shirya jagorancin ƙasarnan ba. Abun da su ke so kawai su ƙwaci mulki su riƙe muƙami.”

“Yanzu ga shi sun samu mulkin sun samu muƙamin amma basu san me za suyi da shi ba,”

Ya ƙara da cewa “Kuma rayuwa tana ƙara tsanani ga ƴan Najeriya da dama saboda gazawar su,”

Tsohon gwamnan ya yi kira ga jam’iyun adawa da su haɗa hannu su tabbatar cewa APC ta faɗi zaɓe mai zuwa.

More from this stream

Recomended