Zulum Ya Yi Alhini Bayan Fashewar Bama-Bamai Ta Kashe Mutane 8 a Borno

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana alhini da takaicinsa bayan wata fashewar bama-bamai da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka dasa ya kashe mutane takwas tare da jikkata wasu 21 a hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

Fashewar, wadda aka yi zargin na’urar fashewa ce ta zamani (IED), ta auku ne a ranar Asabar, inda ta auka wa wasu motoci masu dauke da fasinjoji da ke tafiya a kan hanyar.

Rahotanni sun bayyana cewa cikin wadanda suka jikkata, mutum 14 sun samu munanan raunuka, yayin da sauran 7 suka samu sauki bayan samun kulawa a Asibitin Musamman na Jihar da ke Maiduguri.

“Abin takaici ne cewa haka ta faru a yanzu. Fiye da shekara guda ba mu fuskanci harin IED ba,” in ji Zulum.

Ya kara da cewa an rufe hanyar da lamarin ya faru tsawon wata guda kafin faruwar harin.

Gwamnan ya jajanta wa iyalan wadanda suka mutu tare da yin kira ga rundunonin soji da sauran jami’an tsaro da su kara sanya ido da kai dauki don hana faruwar hakan a gaba.

“Dole ne mu kara matsa kaimi wajen tsaro. Ina rokon jami’an tsaro su inganta bincike da sa ido a wannan hanya,” in ji shi.

Ya kuma yi alkawarin kara karfafa matakan tsaro na cikin gida, ciki har da tallafa wa dakarun Civilian Joint Task Force (CJTF) da matasan sa-kai da ke fafutukar yaki da ‘yan ta’adda.

More from this stream

Recomended