Wasu matasa a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun gudanar da zanga-zanga a ranar Talata a sakatariyar gwamnatin jihar, bayan harbin bindiga daga hannun wani dan sanda ya kashe wani dalibi da ke kan hanyarsa ta zuwa rubuta jarrabawar WAEC.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar Talata a titin kasuwar Gbagi, inda harsashin da aka harba bisa kuskure ya harbi dalibin.
Ganau sun ce marigayin yana tare da mahaifinsa da wani daga cikin ‘yan uwansa lokacin da lamarin ya faru.
Bincike ya nuna cewa dan sandan da ya harba harsashin na kokarin bin sahun wani da ake zargi da aikata laifi ne, kafin harsashin ya sauka kan dalibin.
An garzaya da wanda aka harba zuwa Asibitin Welfare, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa da isarsu.
Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Ibadan Bayan ‘Yan Sanda Sun Harshe Wani Dalibi Da Yake Zana Jarrabawar WAEC
