Zan kawo karshen yajin aikin ASUU a ranar da zan shiga ofis – Atiku

Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban Najeriya karkashin jam’iyar PDP, ya yi alkawarin kawo karshen dogon yajin aikin da kungiyar malaman jami’a ta ASUU take yi a ranar da ya fara shiga ofis a matsayin sabon zababben shugaban kasar Nijeriya.

Atikun ya bayyana hakan yayin da ake gabatar da wanin taron bayar da lambar girmamawa mai taken “Silverbird Man of the Year” a jihar Legas.

A dangane da jawabin Atiku, yajin aikin wanda ya haramta wa daliban jami’ar kasar nan karatu na kusan tsawon watanni hudu abin kunya ne, saboda haka shi zai fara maida wa hankali a matsayinsa na shugaban kasa idan aka zabe shi a zaben 16 ga watan Fabrairun wannan shekarar.

Atiku ya ce: “Na yi matukar kaduwa kasancewar a yanzu haka da nake magana, dalibanmu na fadin kasar nan suna zaune a gida ba sa karatu saboda yajin aikin kungiyar ASUU wanda muhawar kusan naira biliyan 60 da aka kasa warwarewa ta janyo.

“Idan na samu aikin da nake nema, abun da zan fara a ranar farko shi ne kawo karshen wannan yajin aikin mai cike da abin kunya, sannan in maida dalibanmu karatunsu.”

Atiku Abubakar ya kara da fadin, “Bayan nan zan kuma rubanya kudin da gwamnatin Nijeriya take kashe wa ilimi har sau uku, daga kaso 7 bisa dari na kasafin kasar zuwa 20, ba ma 15 ba da UNESCO ta tsara.

“Na gane darajar da ilimi zai iya kawo wa mutum da kasa. Amma sama da hakan ma, ina so ko wanne yaro a Nijeriya ya samu damanmakin da na samu.”

More News

An sallami ƴan sanda uku daga bakin aiki kan isan wani dalibi

Rundunar ƴan sandan jihar Kwara ta ce ta sallami jami'an ta uku da aka samu suna da hannu a kisan wani dalibin makarantar kimiya...

Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da ƴan ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami'an ƴan sanda da kuma sojoji suna ɗaukar bindigogi daga...

Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatan jihar.Sanwo-Olu ya bayyana hakan...

Sama da mutane 100 aka tabbatar sun mutu a gobarar hatsarin tankar mai a Jigawa

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 140 a hatsarin gobarar tankar mai da ta faru a garin Majia dake kan...