
Wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya kuma makusantan shugaban kasar sun bayyana rashin jin dadinsu game da ihun da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da ya gabatar da kasafin kudin 2019.
A ranar Laraba ne shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin N8.83tr ga majalisar dokokin kasar.
Sai dai masu wasu sun rinka ihu domin nuna adawa da wasu bayanai na shugaban, yayin da wasu suka rinka sowa domin nuna masa goyon baya.
Honourble Farouk Adamu Aliyu, jigo ne a jam’iyyar ta APC mai mulkin Najeriya, kuma tsohon shugaban marasa rinjaye ne a majalisar wakilan Najeriya, ya ce ya yi mamakin ‘tsaurin idon’ da ya ce an yi wa wa shugaban kasar.
Tsohon dan majalisar ya ce ‘ya’yan jam’iyyar APC za su dauki mataki a siyasance ta hanyar wayar wa al’umma kai domin kada su sake zaben wadanda suka yi wa shugaban ihu.
Ya shaida wa BBC cewa bai kamata a ce ‘yan majalisar sun dauki irin wannan mataki kan shugaban kasar ba.
Ya kuma yi zargin cewa shugabannin majalisar wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa su ne ke kokarin tozarta shugaban na Najeriya.
Hon Faruk ya kuma ce ‘yayan jam’iyyar APC da suka rinka sowa domin nuna goyon baya ga shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari sun yi ne domin murkushe aniyar ‘yayan jam’iyyar adawa ta kunyata shugaban.