A yau ne ake sa ran kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci kan shari’un zaben gwamna na jihohin Kano da Sokoto.
Wasu da ba su gamsu da yadda zaben ya kasance ba ne dai suka shigar da kara gaban kotun suna kalubalantar sakamakon da hukumar zaben kasar INEC ta bayyana a jihohin.
Hukuncin kotun na yau dai shi ne raba gardama a takaddamar da ake yi kan halattacen gwamnan Kano tsakanin Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC da hukumar zabe INEC tace shi ya lashe zabe, da kuma Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP dake kalubalantar nasara ta Ganduje.
A Sokoto ma kotun za ta raba gardama tsakanin Aminu Waziri Tambuwal na jam’iyyar PDP dake kan kujerar yanzu haka da kuma Ahmad Aliyu na jami’iyyar APC da ke kalubalantar nasarar da INEC ta ce Tambuwal din ya samu.
A watan Maris din bara ne INEC ta bayyana Ganduje na Kano da Tambuwal na Sokoto a matsayin wadanda suka lashe zaben watan Maris, bayan an yi zabe karo na biyu kasancewar zaben zagaye na farko bai kammala ba, wato dai ya zama inconclusive, abinda Abba da Ahmed Aliyu suka kalubalanta.
Tun a makon jiya ne dai kotun ta shirya bayyana hukunci kan jihohin na Kano da Sokoto tare da wasu jihohin, to amma wasu dalilai sun sanya kotun dage yanke hukuncin zuwa yau.
A shari’a da aka yi ta kotun kararrkin zabe ta jiha dai Ganduje ne ya samu nasara a Kano, Tambuwal ya samu nasara a Sokoto, sannan sun kara samun nasara a kotun daukaka kara a Kaduna.
Duka masu karar dai sun garzaya kotun kolin ne sabo da rashin gamsuwa da hukuncin da kotunan baya suka yanke.
A yanzu matakin na Kotun Koli shi ne zai kasance na karshe a ja-in-jar da ake yi kan kujerun gwamnonin jihohin.
Kuma dole ne a karbi hukuncin a kuma yi aiki da shi ko da kuwa ba a samu yadda ake so ba.
Rashin tabbas, da rashin sanin mai zai faru ya sa magoya bayan wasu masu takaddamar a kotu ta koli suka dukufa da addu’ar neman nasara ga gwanayensu.
A makon da ya gabata ne dai Kotun ta Koli ta yanke hukunci kan shari’ar zaben jihar Imo inda ta sauke gwamnan jihar na lokacin Emeka Ihedioha ta ce kuma a rantsar da Hope Uzodinma, hukuncin da ya rikita lisafin ‘yan kasar da dama, musamman ma ‘yan siyasa.
Hukuncin na jihar Imo ya kara haifar da rashin tabbas kan abinda zai iya faruwa a kotun a yau, kuma ya kara tabbatar da karin maganar nan da ake cewa shari’a mace ce mai ciki ba a san me za ta haifa ba.