Yobe: Boko Haram ta kai mummunan hari a wani ƙauye

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kauyen Ngurokayya da ke karamar hukumar Geidam a jihar Yobe a ranar Talata.

Har yanzu dai ba a san adadin wadanda suka mutu ba yayin da cikakkun bayanai ke ci gaba da fitowa.

Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dokta Mohammed Goje, ya tabbatar da harin a kauyen a wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Facebook da aka tabbatar.

“Wadanda ake zargin ‘yan NSAG ne sun kai hari kan wata al’ummar kan iyaka, wani kauye mai suna Ngurokayya da ke unguwar Kusur Damakarwa a karamar hukumar Geidam.

“Ngurokayya yana da nisan kilomita 10 zuwa Gumsa. An yi asarar rayuka tare da jikkata wasu da dama, kuma sun kona garin kuma an samu rahoton cewa mutane na tserewa daga garin zuwa wani wuri mafi aminci,” in ji shi.

A cewarsa jami’an tsaro suna da cikakken bayani kuma ana ci gaba da daidaita al’amura.

More News

Dakarun Najeriya sun cafke wasu ƴan’aiken ƴanbindiga a Kaduna

Sojoji sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da kaiwa 'yan bindiga sakonninsu a kasuwar ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia a...

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴanbanga sun sake kawar da wani ƙasurgumin ɗanbindiga

Rahotanni da ke fitowa daga Arewa maso Yammacin Najeriya na nuna cewa an yi nasarar kawar da wani fitaccen dan bindiga a jihar Zamfara,...

Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan...