Yau za a gudanar da zaben fid da gwani a Zamfara

Gwamnan Zamfara

A jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, a yau ne ake sa ran za a yi zaben fidda-gwani na masu neman takarar gwamna a karkashin jam`iyyar APC.

Sau uku ana sanya ranar zaben ana dagewa saboda wasu matsaloli.

Amma dukkan bangarorin da ke rikici da juna a wajen wannan zaben sun sasanta da juna – kama daga bangaren gwamnatin Zamfara zuwa bangaren gungun wasu ‘yan takara su takwas.

Shugaban kwamitin zaben fid da gwanin, Dr. Abubakar Fari ya kawar da duk wata shakka game da gudanar da zaben ranar Laraba:

“Mun warware dukkan wasu matsaloli da ke son dabaibaye gudanar da zaben, daga safiyar Laraba za a yi zabe a dukkan matsabun jihar Zamfara.
Tun da farko dai gwamna Abdulaziz Yari na jihar ya kafe cewa ba za a guudanar da zaben fid da gwanin ba, domin wasu dalilai da suka hada da cin fuska da kuma rashin tuntubarsa da ya ce kwamitin shirya zaben bai yi ba.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...