Wata yarinya ƴar shekara 16 mai suna Joy Afekafe ta samu hukuncin daurin rai da rai a gidan gyaran hali, bayan samunta da laifin kashe wata malamar jami’a a Minna, tun tana da shekara 14.
Mai shari’a Mohammed Adishetu Mohammed na Babbar Kotun Minna mai lamba 4 ne ta yanke hukuncin a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa ta yanke hukunci.
Kotu ta tabbatar da cewa Joy Afekafe da wasu abokanta da ke tsare sun kashe Dr Mrs Funmilayo Sherifat Adefolalu, malamar Jami’ar Fasaha ta Tarayya (FUT) da ke Minna, ta hanyar soka mata wuka sau da dama.
Mai shari’a Mohammed ya ƙara da cewa lauyoyin gwamnati sun tabbatar da laifin kisan kai mai ɗauke da hukuncin kisa da kuma fashi da makami. Sai dai saboda dokar jihar Neja ta 1989 a sashen 221 na kundin Penal Code, wanda ke hana yanke hukuncin kisa ga wanda bai kai shekara 18 ba a lokacin da aka aikata laifi, kotu ta maye gurbin hukuncin kisa da daurin rai da rai.
Baya ga daurin rai da rai da aka yanke mata kan kisan kai, kotu ta kuma ɗora mata daurin shekaru 10 kan laifin fashi da makami.
An cafke Joy ne bayan binciken da ‘yan sanda suka gudanar wanda ya nuna cewa ita ce tare da abokanta Walex da Smart – waɗanda ke tsare – suka kai wa malamar hari a gidanta.
Yarinya Ƴar Shekara 16 Da Haihuwa Za Ta Sha Hukuncin Daurin Rai Da Rai Bayan Ta Yi Ajalin Malamar Jami’a A Minna
