Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce mulki zai dawo yankinsu na kudu maso yamma idan Buhari ya kammala wa’adinsa na biyu.
A yayin da yake yakin neman zabe a jihar Oyo, Osinbajo ya ce Buhari zai mika wa Yarabawa mulki a 2023 idan har sun mara ma shi baya a zaben 2019, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
“Zaben 2019 ya shafi al’ummar Yarabawa a kudu masu yammaci saboda babbar bukatar yankin a 2023,” in ji shi.
Osinanjo wanda ya bi gida gida da kasuwanni da sako a Ibadan da wasu sassan jihar Oyo, ya yi kira ga mutanen yankin su fito domin sake zaben Buhari.
Shugaba Buhari dai ya sha mika ragamar tafiyar da kasa ga mataimakinsa Osinbajo a duk lokacin da zai je jinya kasashen waje.
Kuma yadda Osinbajo ya zartar da daukar wasu matakai kan wasu muhimman al’amurra a kasar, wasu ke ganin ya kama hanyar zama shugaban kasa.
Yana mukaddashin shugaban kasa aka kara farashin litar fetur, sannan shi ya sallami shugaban hukumar DSS, Lawal Daura.
Komawar mulki yankin kudu maso yammaci a 2023 zai dogara ne da samun nasarar Buhari a zaben 2019.