Cutar baƙondoro ta yi sanadin mutuwar yara biyar a unguwar Kanawa da ke Tankarau, Dutsen Abba, a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.
Hakimin unguwar Kanawa, Nasiru Yunusa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa yara biyu daga gida ɗaya sun rasu kimanin kwanaki bakwai da suka gabata.
Yunusa ya danganta mutuwar yaran da rashin amincewar mazauna yankin wajen kai yara allurar rigakafi.
“Fiye da rabin mutanenmu ba sa sha’awar rigakafin yara saboda wasu ra’ayoyi na ƙarya. Amma yanzu da cuta da mutuwa suka shigo, mutane da dama sun fara canza tunaninsu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa akwai wasu yara da ke fama da cutar baƙondoro a cikin al’ummar.
Ya bayyana cewa mafi yawan waɗanda suka kamu da cutar su ne waɗanda iyayensu suka ƙi kai su yin rigakafi.
Hakimin ya kuma koka kan rashin cibiyar lafiya a yankin, yana mai cewa cibiyar lafiya mafi kusa tana da nisan kimanin kilomita bakwai.
“Matanmu na haihuwa a gida saboda babu asibiti ko asibitin ƙananan yara a kusa da mu. Muna roƙon gwamnati ta kawo mana cibiyar lafiya,” in ji shi cikin ƙorafi.
Yara Biyar Sun Mutu Sakamakon Cutar Baƙondoro a Wani Ƙauye na Kaduna
