Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta gurfanar da wani direban mota mai suna Usman Muhammed, wanda ya murkushe wasu mabiya addinin Kirista da motarsa yayin bukukuwan Easter da suka gudana a ranar Litinin.
Lamarin mai ban tausayi ya faru ne a Tashan Gona, karamar hukumar Billiri, inda wata babbar mota dauke da kayan abinci ta kubuce wa direbanta, ta kutsa cikin taron mabiya addinin Kirista da ke dawowa daga wurin ibada.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Buhari Abdullahi, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa an shigar da karar direban mai shekara 28 da haihuwa bisa tuhume-tuhume guda biyu: tukin ganganci da kuma haddasa mutuwa ta hanyar tuki.
Rundunar ‘yan sandan ta yaba da hadin kan jama’a wajen bayar da bayani da goyon baya a lokacin bincike, inda ta kuma bukaci duk wanda ke da karin bayani ya tuntubi shugaban sashen kula da zirga-zirgar ababen hawa na rundunar da ke ofishin ‘yan sanda na yankin Gombe.
An kuma tabbatar wa al’umma cewa za a ci gaba da ba da bayani kan yadda shari’ar ke tafiya a gaban kotu.
‘Yansanda Za Su Gurfanar da Direban Da Ya Halaka Masu Bikin Easter a Gombe
